Martanin Afirka ta Kudu kan korar jakadanta na Amurka
March 15, 2025Afirka ta Kudu ta nuna takaicinta kan matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na korarar jakadanta a Washington Ebrahim Rasool, wanda ta zarga da nuna wa Amurka da Mr Trump kiyayya karara.
Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ne ya sanar da korar a shafinsa na X na ranar Juma'a, yana mai zargin jakadan da cewa 'dan siyasa ne mai nuna wariyar launin fata, lamarin da ya kara rura wutar rikicin diflomasiyya da ya kunno kai tsakanin Washington da Pretoria.
Karin bayani:Amurka ta janye tallafin da take ba wa Afirka ta Kudu
A cikin watan Fabarairun da ya gabata ne Mr Trump ya wallafa wani sako a shafinsa na sada zumunta na Truth Social cewa Amurka ta dakatar da duk wani tallafi da take bai wa Afirka ta Kudu, sakamakon zarginta da kwace gonakin fararen fata na kasar.
Karin bayani:Trump ya yi barazanar katse zuba Jari a Afirka ta Kudu
Wannan dalili ne ya sa shugaba Trump ya sanar da cewa duk wani manomi da aka kwace wa gona, kuma yake fatan koma wa Amurka to zai samu izinin zama 'dan kasar cikin sauki.