Plateau: Sababbin dokoki kan matsalar tsaro
April 17, 2025Karkashin sababbin dokokin dai, gwamnati ta haramta jigilar dabbobi a motoci bayan karfe bakwai na yamma. A wani takaitaccen jawabi da gwamnan ya gabatar ga al'ummar jihar ta Plateau ne, Gwamna Celeb Mutfwang ya ce gwamnati ta haramta kiwon dabbobi a ko'ina cikin jihar da daddare. Haka kuma gwamnati ta saka dokar haramta zirga-zirgar babura, daga karfe bakwai na yammacin zuwa karfe shida na safe.To sai dai wasu al'ummar jihar na ganin kamata ya yi gwamnatin ta mayar da hankali wajen tura isasun jami'an tsaro, zuwa kananan hukumomi da aka gano 'yan bindiga na cin karensu babu babbaka.
A cewar wani dan yankin karamar hukumar Bokkos Mr Felis-Amos Agyambal yanzu haka, 'yan binidgar na kokarin mamaye yankunan saboda dimbin arzikin albarkatun kasa da suke da shi. A jawabinsa gwamnan ya kawo shawarar sarakunan gargajiya tare da kungiyoyin matasa su kafa 'yan banga da za su yi aiki tare da jami'an tsaro, domin kare al'umma daga farmakin 'yan ta'adda. A yanzu haka dai al'umma sun zuba ido ne suga ko sababbin dokokin da gwamnan ya sanar, za su kawo karshen matsalolin hare-haren 'yan bindiga da suka addabi jihar ta Plateau.