Martani kan nadin sabon sarkin Gusau
July 30, 2025Tun bayan rasuwar sarkin gwamnatin jihar Zamfara ta ci gaba da bibiyar al-adar masarautar wajen nada wanda zai gaji marigayin domin ci gaba da gudanar da lamuran masarautar wanda ya bada damar nada dan marigayin, to ko wadanne ka'idoji da ma'auni gwamnatin jihar ta bi wajen nada sabon sarkin ganin akwai wadanda suka nemi sarautar.
Sarakunan gargajiya na da gagarumar rawar takawa wajen ci gaban al'umma a kasar Hausa to ko wacce irin rawa ake sa ran sabon sarkin zai taka ga al'ummar sa?
Al'ummar wannan masarauta ta Gusau musamman matasa na ci gaba da bayyana fatan su ga sabon sarkin
An dai haifi sabon sarkin ne a ranar 11 ga watan December 1977 kuma ya yi karatu mai zurfi a jami'ar Amadu Bello ta Zaria bayan karatunsa na primary da Sakandire a garin Gusau kuma kafin nadin nasa ma'aikacin gwamnati ne a hukumar kula da asibitocin gwamnatin jihar.