Maratani Jamus kan kisan kiyashi a Hula
May 30, 2012Gwamnatin Jamus ta karfafa bukatar warware rikicin kasar Siriya a siyasance. Kakakin gwamnatin Jamus ya ce shugabar gwamnati, Angela Merkel za ta yi amfani da ziyarar da shugaban Rasha, Vladimir Putin zai kawo Jamus kasar a ranar 01-06-2012 ta mika bukatar kara yin matsin lamba ga gwamnatin kasar ta Siriya. Ita kuma ma'aikatar harkokin wajen Jamus karawa ta yi da cewa babu wani dalilin yada jita-jitar daukar matakin soji akan Siriya. Kenan ra'ayin gwamnatin Jamus ya saba wa na shugaban Faransa, Francois Hollande wanda ya ce za a iya daukar matakin soji a sakamakon kisan kiyashin da aka yi wa farar hula a garin Hula. Kasar Rasha ita kuma ta yi fatali da bukatar tafka muhawara akan Siriya a komitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya. Wasu kafafe da ke da alaka da 'yan adawar kasar ta Siriya sun bayyanar da videon na gawawwakin mazaje 13 da aka kashe a lardin Dair as Saur da hannyensu daure a bayansu. 'Yan adawar dai suka ce gawawakin na wasu sojoji ne da suka yi yunkurin sauya sheka.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Yahouza Sadissou Madobi