SiyasaTarayyar Rasha
Manzon Amurka ya isa Moscow kan sulhunta yakin Ukraine
August 6, 2025Talla
Manzo na musamman da shugaban Amurka Donald Trump ya nada domin shiga tsakani a yakin Rasha da Ukraine Steve Witkoff ya isa birnin Moscow a wannan Laraba, inda zai gana da mahukuntan kasar kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Tass ya ruwaito.
Ziyarar ta Steve Witkoff na zuwa ne yayin da ya rage kwanaki biyu kafin karewar wa'adin kwanaki 10 da shugaba Trump ya ba wa Rasha domin dakatar da kai wa Ukraine farmaki ko kuma ta fuskanci karin haraji mafi tsauri.
Danganta dai a tsakanin Moscow da Washington ta dau dumi a makon da ya gabata, lamarin da ya kai shugaban Amurka Donald Trump ga tura jiragen ruwan yaki guda biyu dauke da makaman nukiliya bayan takun saka da suka yi ta yanar gizo da tsohon shugaban Rasha Dmitry Medvedev.