Manyan kasashen Turai sun zargi Iran a kan Nukiliya
August 28, 2025Talla
Wadannan kasashe uku sun cika barazanar da suka yi, inda suka fara aiwatar da matakin dawo da takunkumin duniya kan Iran a gaban Majalisar Dinkin Duniya.
Dawowar takunkumin, na a cikin yarjejeniyar da Iran ta rattaba hannu a kanta a shekarar 2015 tare da mambobin dindindin guda biyar na kwamitin tsaron MDD da kuma Jamus.
A halin yanzu, tattaunawa don tabbatar da cewa Tehran ba ta neman mallakar makamin nukiliya ta tsaya cik, bayan Washington ta fice daga yarjejeniyar a ƙarƙashin shugabancin Donald Trump, sannan Isra’ila ta kai hare-hare na kwanaki da dama kan muhimman cibiyoyin Iran.
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi Allah-wadai da wannan mataki na Turawa, tana cewa “ba shi da hujja kuma ba bisa doka ba ne.