Man fetur a Jamhuriya Nijar
November 17, 2011Addadin man fetur da Nijar ta mallaka a ƙarƙashin ƙasa? Nawa ne mattatar Zinder za ta iya tacewa ko wace rana?Kuma idan Nijar ta fara saida wannan mai a kasuwanin ƙetare da addadin kuɗi nawa ne aljihun gwamnati zai ƙaru? kuma wane amfani tallaka zai ci daga cikin wannan albarkatun mai ?
Don samun amsar wannan tambaya na tuntuɓi Illiyasu Bubakar daga daga shugabanin ƙungiyar nan mai zaman kanta wato ROTAB wadda ke gwagwarmayar ganin talaka ya ci amfanin albarkatun ƙarƙashin ƙasa da Nijar ta mallaka.Na yi masa tambayayoi da dama domin faɗakar da masu sauraro game da man fetur da Nijar ta fara haƙowa kuma za ta fara tacewa a cikin wannan wata,a matatar mai dake jihar Zinder.
Za ku iya sauraran wannan hira idan kuka latsa kasa:Man fetur a Jamhuriya Nijar
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu