Mambobin gwamnatin Jamus daga kawancen CDU/CSU
Bangaren CDU da CSU ya fitar da jerin mutanen da za su kasance ministoci a gwamnatin Tarayyar Jamus, inda Friedrich Merz na jam'iyyar CDU zai jagoranci gwamnati. Akwai sunayen da suka ba da mamaki.
Shugaban Gwamnati: Friedrich Merz (CDU)
Friedrich Merz mai shekaru 69 da haihuwa kuma masanin dokoki na fuskantar kalubale a ciki da wajen kasar. Tattalin arzikin Jamus na cikin mawuyacin hali, kana jam'iyyar AfD mai kyamar baki na kara tasiri. Jagoran jam'iyyar CDU na son zaburar da tattalin arzikin da dakile shigar bakin haure. Gaba daya yana da aiki domin ba a taba samun shugaban gwamnati maras farin jini irin Friedrich Merz ba.
Ma'aji: Thorsten Frei (CDU)
Mai shekaru 52 da haihuwa, Thorsten Frei ya kasance makusancin Friedrich Merz mai tasiri. Yana majalisar dokokin Bundestag tun shekara ta 2013, inda a baya ya taka rawa a siyasar jihar kudancin Jamus. Mutum ne da ke cikin fara'a a kowane lokaci kuma ya iya kalami. A matsayinsa na Ma'aji, aikin da zai saka a gaba shi ne fahimtar matsalolin da za su tunkari Friedrich Merz domin ya magance su.
Ministan Harkokin Waje: Johann Wadephul (CDU)
Mai shekaru 62 da haihuwa, Johann Wadephul na majalisar dokokin Bundestag tun a shekara ta 2009, inda yake mayar da hankali kan harkokin waje. Yana da digirin digirgir a bangaren dokoki, kana tsohon soja ne da ke sara yana duba bakin gatari. Yana dasawa da Friedrich Merz. Mutanen biyu za su gane wa juna kuma ma'akatar harkokin waje bayan shekaru 60, ta sake dawowa hannun jam'iyyar CDU.
Ministan Harkokin Cikin Gida: Alexander Dobrindt (CSU)
Alexander Dobrindt, dan siyasa na jam'iyyar CDU ya kasance ministan sufuri a lokacin mulkin Angela Merkel. Yanzu a matsayin ministan cikin gida mai shekaru 54 da haihuwa, yana neman ganin an dakile shigar bakin haure cikin Jamus, wajen hana bakin hauren tsallaka iyakar kasar, da ma hana wa iyalansu samun damar shiga gami da korar 'yan Siriya da Afghanistan daga Jamus.
Ministar Tattalin Arziki da Makamashi: Katherina Reiche (CDU)
Mai shekaru 51 da haihuwa Katherina Reiche, ta sake dawowa harkokin siyasa. Tana shekaru 25 ta zama mamba a majalisar dokokin Bundestag, har ta kai mukamin Sakarariya a Majalisar. A shekara ta 2015 'yar siyasar daga Jamus ta Gabas ta tsunduma harkokin kasuwanci. Ta jagoranci wani kamfani mai bai wa gwamnatin tarayya shawara a shekara ta 2020.
Ministar Bincike da Fasaha da harkokin samaniya: Dorothee Bär (CSU)
Dorothee Bär mai shekaru 47, tana majalisar dokokin Bundstag ne tun a shekara ta 2002 kuma ta kasance daya daga cikin mataimakan shugaban majalisa a bangaren hadakar CDU/CSU. Tun shekara ta 2017 tana cikin mataimakan shugabannnin jam'iyyar CSU. Daga 2018 zuwa 2021 lokacin mulkin shugabar gwamnatin Angela Merkel, an nada Dorothee Bär a matsayin kwamishinar hukumar fasahar zamani.
Ministan fasahar zamani: Karsten Wildberger
Sunan Manaja Karsten Wildberger babban abin mamaki ne. Yana da digirin digirgir a fannin kimiyyar "Physics" kuma ya yi aiki da kungiyoyin kasa da kasa. Mai shekaru 56 da haihuwa ya jagoranci babban kamfanin kasashen Turai na kayan laturoni. Har zuwa yanzu ya kasance mai neman taimaka wa jam'iyyar CDU.
Ministar Lafiya: Nina Warken (CDU)
Nina Warken na cikin 'yan majalisar dokokin Bundestag da sunanta ya ba da mamaki a matsayin minista. Mai shekaru 45 da haihuwa ta shiga jam'iyyar CDU tun lokacin da take makaranta tana karanta ilimin dokoki kuma; tana majalisar dokokin Bundestag tun shekara ta 2013. Sai dai ta fi mayar da hankali ne kan manufofin cikin gida. Yanzu lauyar za ta mayar da hankali kan manufofin kiwon lafiya.
Ministar Ilimi da harkokin iyali: Karin Prien (CDU)
Karin Prien ta kasance guda daga cikin 'yan siyasa masana harkokin ilimi a jam'iyyar CDU. Mai shekaru 59 da haihuwa, tana rike da mukamun ministar ilimin jihar Schleswig-Holstein tun a 2017. Prien na da ra'ayi kuma ba ta jin shakkar muhawara. A kasar Netherlands aka haife ta har ta girma, inda kakanninta suka tsere saboda mulkin 'yan Nazi na Jamus a shekarun baya.
Ministan aikin gona: Alois Rainer (CSU)
"Yanzu za mu sake samun yabanya" - da wannan kalaman jagoran jam'iyyar CSU-Markus Söder ya gabatar da sabon ministan aikin gona Alois Rainer mai shekaru 60 da haihuwa wanda yake da kwarewa kan aikin kiwo wanda iyalansa ke yi tsawon shekaru a yankin Bavaria na Jamus. Ya shiga majalisar dokoki ta Bundestag a shekara ta 2013, inda yake bangaren kasafin kudi da sufuri.
Ministan Sufuri: Patrick Schnieder (CDU)
Patrick Schnieder a matsaiyn ministan sufuri zai samu abin da abokan aikinsa suke fata na kudi mai yawa. Akwai makudan kudaden da aka ware Euro milyan dubu 500 musamman domin inganta harkokin sufuri. Mai shekaru 56 da haihuwa kuma lauya daga yammacin Jamus, ya kasance dan majalisar tarayya tun shekara ta 2009.
Karamin ministan al'adu da yada labarai: Wolfram Weimer
Mawallafi kuma dan jarida Wolfram Weimer, zai bai wa shugaban gwamnati Friedrich Merz kwarin gwiwa a bangaren masu ra'ayin mazan jiya. Mai shekaru 60 da haihuwa yana da digirin digirgir a bangaren tarihi, inda ya rubuta littattafai da dama da suka hada da "Manufofin masu ra'ayin mazan jiya". Ya yi aiki da jaridun Frankfurter Allgemeine Zeitung (FAZ) da Die Welt.