Mali ta tsare tsohon Firanministan kasar
August 2, 2025Kotun na tuhumar tsohon Firaministan kasar, Moussa Mara da laifin wallafa wani sakon suka ga gwamnatin mulkin sojin kasar a shafinsa na dandalin sada zumunta. An dai gayyaci Mara a lokuta da dama domin ya amsa tambayoyi kan sakon da ya wallafa a ranar 4 ga watan Juni na nuna goyon baya ga 'yan adawa da ake tsare da su. A yanzu dai kotu na tuhumarsa da laifin yada labaran karya da kuma zubar da mutuncin kasar, inda aka dage sauraron shari'ar zuwa ranar 29 ga watan Satumbar wannan shekarar.
Karin bayani: Assimi Goita ya rusa kungiyoyi da jam'iyyun Siyasar kasar Mali
Kawo yanzu dai gwamnatin mulkin sojin kasar ba ta ce uffan ba a kan lamarin. Mara dai na daga cikin 'yan kasar da suka fito fili suka nuna adawa da matakin majalisar mulkin sojin kasar karkashin Assimi Goita, wadanda suka hada da rusa jam'iyyun siyasa inda sojoji za su ci gaba da jan ragamar kasar na tsawon shekaru biyar kafin zabe.