Mali ta ce babu sojojin Rasha a kasar
December 25, 2021Talla
A tsakiyar wannan satin da ke karewa ne, kasashen yammaci na Turai 15 ciki har da Kanada da Jamus da Faransa da ma Birtaniya suka bayyana takaicinsu bayan samu labarin sojojin Rasha sun fara isa Mali.
Kasashen na ganin Rasha ba za ta yi maganin halin da kasar da ma yankin Sahel ke ciki ba. Kuma Mali na karkatar da kudaden kasar da ba su ishi al'umma ba ga daukar sojin haya.
Ana ci gaba da nuna damuwa a game da yadda wannan gwamnatin rikon kwarya karkashin jagorancin kanal Assimi Goita ke tafiyar da batu na matsalar tsaro a kasar ta Mali.