Mali ta kama wani dan Faransa kan zargin kitsa juyin mulki
August 15, 2025Mahukuntan Mali sun sanar da cafke wani Bafaranshe da suke zargi da yin aiki da hukumar leken asirin Faransa, tare kuma da zargin wasu kasashen ketare da hannu a yukurin kawo cikas ga hukumomin gwamnatin milkin sojan kasar.
A cikin wata sanarwa da aka yada a kafar talabijin din kasar a daren jiya Alhamis, gwamnatin ta Mali ta ce baya ga kasar Farasar, ta kuma kama wani gungun sojoji 55 da ke neman tayar da zaune tsaye bayan wani yunkurin juyin mulki bai yi nasara ba.
Sanarwar ta kuma ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin zakulo karin wadanda ke da hannu a wannan lamari tare da tabbatar da kama wasu manyan janar guda biyu ciki har da tsohon gwamnan yanki Mopti Janar Abass Dembélé wanda aka sauke daga mukaminsa a baya-bayan nan.
Dama dai kwanaki biyu da suka gabata hukumar yaki da ta'annati da dukiyar kasa ta Mali ta kama tsohon firaministan kasar Choguel Kokalla Maïga da wasu tsoffin abokan aikinsa domin bincikarsu kan zargin aikata almundahana.