Damuwa kan jibge sojojin Rasha a Mali
November 12, 2021Talla
Ministan harkokin kasashen wajen na Faransa Quai d'Orsay na mayar da martani ne, dangane da tattaunawa kan jibge rundunar yakin Rasha ta Wagner a kasar da ke yankin Sahel da kuma ke fama da rikici. A cewarsa, hakan zai iya janyo rikici a kasar ta yankin yammacin Afirka da kuma muradan Faransa da kawayenta da ke yakar 'yan ta'adda a Sahel.