SiyasaAfirka
Mali da sojojin Rasha na Wagner sun halaka Fulani da dama
July 22, 2025Talla
Kungiyar kare hakkin 'dan adam ta Human Rights Watch ta fitar da wani rahoto da ke cewa dakarun Mali da sojojin hayan Rasha na Wagner sun kashe dururuwan kabilar Fulani makiyaya a wannan shekara ta 2025.
Karin bayani:Matsayin sojojin hayan Rasha a Afirka
Rahoton ya bayyana cewa Mali da sojojin hayan Rasha na Wagner sun halaka mutanen ne sakamakon zarginsu da hada kai da masu ikirarin jihadi a kasar da ke yammacin Afirka tare da taimaka musu da bayanan sirri da kuma mayaka.
Karin bayani:Mali za ta binciki sojojinta da ake zargi da kisan mutane 24
Kungiyar ta tattara alkalumanta ne ta hanyar tattaunawa da mutane 29 ta wayar tarho wadanda suka tabbatar da afkuwar lamarin, ciki har da shaidun gani da ido 16 daga watan Fabrairu zuwa Mayun 2025.