Nijar: Malaman makaranta na korafi
March 4, 2025Kungiyoyin na Dynamique da COSEFP sun yin hannunka mai sanada ga gwamnatin, ta hanyar cewa ana yin biris da bukatun da suka gabatar. Koda yake gwamnatin ta dauki alkawrin duba matsaloli nasu, tun a farkon watan Disambar shekarar da ta gabata ta 2024 da ya sa suka dage wani yajin aiki da suka kudiri a niyar yi domin ba da damar tattaunawa. Sai dai kuma duk da haka gamayyar kungiyoyin na Dynamique da COSEFP a Nijar sun ce akwai halin ko in kula cikin lamarin na gwamnati dangane da matsalolin malaman makarantun, wanda ganin hakan ne suka fitar da sanarwar a cewar Issoufou Cherif mai magana da yawun gamayyar kungiyoyin kana magatakardan kungiyar malaman makaranta ta CYNACEB. Sanarwar ta gamayyar kungiyoyin malaman makarantar ta tunatar da yadda a baya suka gana da firamninista domin sanar da shi halin da suke ciki da kuma zama da minista mai kula da harkokin ilimi da horo, inda kowa ya aminta da daukar kwararan matakai wajen shawo kan matsalar.
Amma a cewarsu har yanzu babu wani katabus daga bangaren gwamnati, wanda hakan ta sanya suka kira magoya bayansu su yi kokowar kwatar 'yanci. Jariri Labo Seidou shi ne magatakardan kungiyar malaman makaranta na sakandire, kuma daya daga cikin jagororin wata gamayya da kungiyoyin malaman makaranta da ake kira tsarin tuntubar juna na kungiyoyin kula da harkokin ilimi da su ba sa cikin wannan sanarwa. Sai dai ya ce a rinka sara ana duba bakin gatari daga kowa ne bangare, domin kar a bai wa makiya dama a wannan lokaci da ake bukatar cikakken hadin kan 'yan kasa. A cewar gamayyar kungiyoyin malaman makarantar na Dynamique da COSEFP, sun yi haka ne domin al'umma na kasa da sauran magoya bayansu su shaida cewa sun yi nasu iyakar kokarin ganin ba a kai ga cecekuce ba amma ga dukkan alamu tunaninsu bai zo daya da na gwamnatin ba. Duk kokarin DW na jin ta bakin ofishin ministan ilimi da horo na kasar ta Nijar ya ci tura. Da farko sun ce a jira kafin daga bisani su ce, babu wani bayani da za su yi a yanzu kan sanarwar malaman makarantar.