Tasirin nonon uwa ga jarirai
August 5, 2025Majalisan Dinkin Duniya ta kebe ranar 1 zuwa 7 na watan Agustan na kowace shekara a matsayin makon fadakarwa kan shayar da nono uwa. Sai dai kamar bikin na bana na zuwa ne lokacin da iyalai masu yawa ke fuskantar matsalar abinci mai gina jiki sakamakon tsadar rayuwra da ake fuskanta a Najeriya da sauran kasashen masu tasowa. Wannan batu da ma shawarwarin da likitoci ke bayar wa iyaye matan da ke fusknatar karancin ruwan nonon shayar da jariransu.
Taken bikin wannan shekara shi ne ba da fifikon shayarwa da nonon uwa yana gina ingantaccen jikin dan adam.
Karin Bayani: Kamaru: Haramta tallata abinicn jarirai
Wannan mako da majalisar dinkin duniya ta kebe na da manufar jaddada bada fifikon shayar da nonon uwa domin muhimmancinsa ga yara saboda yake gina ingantaccen jikin dan Adam da kuma ba shi kariya da karfafa lafiyar kwakwalwa.
Bikin ranar shayar da nonon uwa na wannan shekara na zuwa ne a lokacin da iyaye masu shayarwa da dama a Najeriya ke fuskantar matsalar yunwa abin da ke zama kalubale a gare su wajen shayarwa.
Masana lafiyar kamar Dr Jilo Jika ya bayyana muhimancin shayar da nonon uwa ga yara, musamman ganin shi ne jigo abin da yara suke bukata lokacin da suke jarirai. Rashin cin abinci ga mata masu shayarwa wata babbar matsala ce ga yara a cewar masana, duba da yadda rashin shayarwa ke haifar da cutuka ga yara musamman yadda yara ke samun karancin sinadarai masu gina jiki.