Makamai dubu 178,000 sun bace a Najeriya
February 13, 2025Wani rahoto na babban mai bincike Najeriyar ne dai ke neman jawo takaddama tsakanin majalisar dattawa ta kasar da rundunan 'yan sandan Najeriyar bisa bata na makamai a rumbunan 'yan sandan Najeriya.
Rahoton dai ya ce akalla makamai dubu 178,459 ne sukai batan dabo a tsakanin shekara ta 2018 zuwa 2020 a rumbunan 'yan sandan. Makaman kuma da suka hada da manyan bindigogikusan 4,000.
To sai dai kuma 'yan sandan sun ce da akwai alamun gishiri cikin batun batan na makamai da ta ce ko dai an kashe jami'anta ne kafin kwasarsu, ko kuma an kai hari a rumbuna na makaman aka kwashe su.
Sakaci cikin batun tsaro ko kuma kokari na aikata laifi ,ko a watan Oktoban bara dai alal ga misali, babban mashawarcin tsaron kasar Nuhu Ribadu ya ce da dama a cikin makaman da masu laifi ke amfani da su a Najeriyar dai sun fito ne daga rumbunan makamai na gwamnatin kasar.
To sai dai kuma a mafi yawa na lokaci kuma a tunanin Mohammed Indabawa da ke zaman tsohon kwamishinan 'yan sanda a rundunar 'yan sadan Najeriyar, batun sai da makamai ga masu aikata laifin na zaman na kurar baya cikin tunanin 'yan sanda a kasar.
Tarayyar Najeriyar dai ta dauki lokaci tana dora batun tsaro na kan gaba cikin kasafin da kan ci dubban miliyoyi na daloli cikin batu na makamai, ba kuma tare da kai wa ga kwalliya biyan kudi na sabulu ba.