Majalisar dokokin Nijar ta yi muhauwara game da hana wani ɗan adawa balaguro ƙetare
August 2, 2011A jamhuriyar Nijar majalisar dokokin ƙasar ta kawo ƙarshen zamanta tare da shirya mahawara akan matakin haramtawa wani ɗan majalissar dokoki na ɓangaran adawa balaguro zuwa ƙasashen ƙetare, a yayin da a share ɗaya wata mahawara ta kunno kai tsakanin yan majalisar dokokin ƙasar da wasu ƙungiyoyin fararen hula na ƙasar dangane da wani bashin kuɗi na miliyan 25 da wani banki ya baiwa ko wani ɗan majalisar ƙasar amma a bisa warantin gwamnatin ƙasar. Ministan sadarwa kana mai kula da hulɗa da hukumomin jamhuriyya shi ne ya wakilci gwamnatin ƙasar a cikin wannan mahauwara akan matakin da gwamnatin ƙasar ta Nijar ta ɗauka na haramtawa Honnorable Ibrahim Fakuda wani ɗan majalissar dokoki na ɓangaran adawa yin balaguro zuwa ƙasar Burkina Faso a ƙarshen makon da ya gabata. To amma da ya ke tsokaci a gaban yan majalisar ministan Mallam Salifu Labo Bushe ya kare matakin gwamnatin.
To amma daga nashi ɓangare ƙawancen 'yan majalisar dokoki na ɓangaren adawa ta bakin kakakin su Mallam Mumini Lamiɗo ya nuna rashin gamsuwar sa da amsar ministan.
Shi ko Honnorable Ibrahim Fukoda lamarin ya shafa kai tsaye bayyana matakin ya yi da cewar wani bita da ƙullin siyasa ne.
A share ɗaya wani bashi na miliyon 25 na kudin Cefa da gwamnatin nijer ta shiga gaba wani bankin ya baiwa yan majalisar ƙasar ta nijer ya soma fuskantar suka daga ɓangaren wasu ƙungiyoyin fararen hula na ƙasar.
To amma akan wannan korafi Honarable Sani Abubakar Zilli ya mayar da martani akan sukar da ƙungiyoyin fararen hular ke yi da cewar tsoki burutsu ne kawai.
Da yammacin yau dai ne majalisar dokokin ƙasar ta Nijar ta kawo ƙarshen zaman na ta bayan ta gudanar da mahauwara akan jerin wasu dokoki da gwamnatin ta shigar a gabanta.
Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita: Mohammad Nasiru Awal