Majalisar dokokin Jamus ta zabi Klöckner a matsayin kakaki
March 25, 2025Majalisar dokokin Jamus ta zabi tsohuwar minista mai ra'ayin rikau Julia Klöckner a matsayin kakakinta, inda ta samu kuri'u 382 yayin da 204 suka ki kada mata kuri'a, sauran 31 kuma suka yi rowar kuri'arsu. Sai dai, ana ganin cewar sabuwar majalisar za ta fuskanci kalubale wajen gudanar da aiki bayan da jam'iyyar AfD mai kyamar baki ta samu kusan kashi daya bisa hudu na kujerun Bundestag a zaben da ya gudanar a ranar 23 ga watan Maris na 2025.
Karin bayani: Ya ya kawancen kafa gwamnatin Jamus zai kasance?
Ita dai Klöckner mai shekaru 52 da haihuwa ta yi wa 'yan majalisa alkawarin gudanar da aikinta cikin natsuwa da kwarin gwiwa, kuma ba tare da nuna son kai ba. Amma dai har yanzu, ba a bayyana lokacin da Bundestag za ta zabi sabon shugabar gwamnati ba, saboda shugaban jam'iyyar CDU Friedrich Merz na ci gaba da tattaunawa don kafa gwamnatin hadin gwiwa da SPD ta shugaban gwamnati mai barin gado Olaf Scholz.