An kada wa gwamnatin Scholz kuri'ar yankar kauna
December 16, 2024'Yan majalisa 394 ne suka nuna rashin gamsuwa da ci gaba da zaman Olaf Scholz a wannan mukamin shugaban gwamnati, yayin da guda 207 suka amince da shi. Kada wannan kuri'a ta yankan kauna ya zama wajibi bayan da jam'iyyar FDP da fice daga cikin gwamnatin hadakar da ke tsakaninta da jam'iyyar Olaf Scholz ta SDP da kuma jam'iyyar The Greens.
Tuni tsigaggen shugaban gwamnatin ta Jamus ya gana da shugaban kasa Frank-Walter Steinmeier, domin mika masa shawarar rusa majalisar dokokin kasar da za ta bayar da damar a gudanar da zaben gabanin wa'adi a watan Fabrairu.
A cikin kwanaki 21 ne ake sa ran shugaban kasar zai sanar da amincewarsa kan tsayar da ranar 23 ga watan Fabrairu a matsayin ranar da za a gudanar da babban zaben kasa a kasar ta Jamus. Kafin wannan lokacin ana sa ran Olaf Scholz ya ci gaba da zama mai rikon mukamin shugaban gwamnatin ta Jamus.