Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da hare-hare a Siriya
May 3, 2025Talla
Tun da yammacin ranar Juma'a ne dai aka fara ganin wasu munanan hare-hare a wasu sassan birnin Damascus da ma wasu yankuna na kudanci da tsakiyar kasar ta Syria.
Sabbin hare-haren ranar Asabar kuma sun zo ne sa'o'i kalilan bayan wani da mayakan saman Isra'ila suka kai kusa da fadar shugaban kasar Syria, bayan gargadin a guje wa yankunan da 'yan kabilar Druze din ke a ciki.
Wani rikicin kwanaki uku tsakanin masu goyon bayan gwamnatin Syria da 'yan kabilar Druze da ke rike da makamai, ya ji sanadiyyar mutuwar akalla mutum 100.