Majalisar Dinkin Duniya ta damu kan batun yunwa a Sahel
February 22, 2012Jaridun na Jamus a wannan mako sun gabatar da sharhuna a fannoni da dama da suka shafi nahiyar Afrika, tun daga halin da ake ciki na yunwa a yankin Sahel harv ya zuwa ga rikicin yan tawayen abzinawa a Mali da suka nasarar da yan wasan Zambia suka samu a wasannin cink ofin kwallon kafa na kasashen Afrika a karshen makon jiya.
Jaridar Süddeutsche Zeitung tayi sharhi game da halin da yankin Sahel yake ciki, inda tace miliyoyin jama'a suna fama da yunwa a Afrika. Jaridar ta ambaci kiyasin kungiyar Red Cross ta duniya dake cewa akalla mutane miliyan 14 ne suke fuskantar barazanar rasa rayukan su saboda yunwa a wannan yanki. Idan ba tare da taimakon gaggawa ba, yawan masu fama da yuwa a kasashen Mali, Burkina Faso, jamhuriyar Niger, Chadi da Mauretania har da Senegal zasu kai kimanin miliyan 25, inda a Chadi da Mauretania saboda karancin ruwan sama, kayan gona da aka samu a bana, bai wuce kashi hamsin cikin dari na yadda aka saba samu a kasashen biyu ba. Jaridar tace ana bukatar agaji na adadin kudi dollar miliyan 720, yayin da majalisar dinkin duniya da kungiyar Red Cross ya zuwa yanzu alkawarin da suka samu bai wuce misalin dollar miliyan 135 ba.
Yayin da Mali take fama da matsalar karancin abinci, sai kuma gashi kasar ta fada rikicin yan tawaye Abzinawa wadanda tun daga tsakiyar watan Janairu suke ci gaba da kisan jama'a a yankunan arewacin kasar. Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tace wannan tawaye ba haka nan kawai ya tashi ba, saboda akwai yiwuwar hannun kungiyar al-Qaeda ta arewacin Afirka a cikin sa. Ya zuwa yanzu, inji jaridar, yan tawaye na kungiyar MNLA sun kashe sojojin gwamnati fiye da 100, tare da farar hula masu yawan gaske. Ita kanta gwamnatin Mali tace kungiyar MNLA tana da hadin kai da kungiyar al-Qaeda ta arewacin Afirka, wato kungiyar Aqmi. Ministan taimakon raya kasashen ketare na Faransa, Henri de Raincourt da ya kai ziyara a Mali, yace irin rashin imanin da kungiyoyin biyu suka yi a yankunan arewacin Mali, abin baya faduwa, sai wanda ya gani. Rikicin na arewcin Mali ya haddasa kwararar yan gudun hijira masu yawa zuwa kasashe makwabta.
Jaridar Berliner Zeitung a wannan mako, ta tabo wani yakin da tace duniya ta manta dashi. Wannan yaki kuwa na gudana ne a tsaunukan Nuba na kasar Sudan, tsakanin yan tawayen Nuba na kungiyar SPLA-N da gwmanatin kasar Sudan. Shi kansa wannan yanki da yan kabilar Nuba suke yi na yantar da kansu daga Larabawa na arewacin kasar da suka mamaye su, an yi shekaru daruruwa ana yin sa. Lokacin da kungiyar SPLA a shekara ta 2005 ta sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tareda gwamnati a Khartoum, yan kabilar Nuba suka balle daga kungiyar suka sanya wa kansu suna SPLA Nuba, suka kuma ci gaba da yaki kan gwamnatin. Jaridar Berliner Zeitung tace yanzu dai babu sauran wanda ya maida hankalin sa ga wadanan tsaunuka, ko duba abin dake gudana a bayan su, maimakon haka, duk an zura idanu ne game da makomar sabuwar kasar Sudan ta kudu da ta sami yancin ta bayan ta balle daga sauran kasar ta Sudan a baya-bayan nan.
Ranar Lahadin da ta wuce, yan wasan kwllon kafa na Zambia suka sami nasarar daukar kofin kasashen Agfrika a wasnnin dfa aka kammala a Gabon da Equatorial Guinea. Dangane da hjaka, jaridar Neue Zürcher Zeitung tace nasarar da yan wasan na Zambia suka samu, ta zama girmamamaye ga yan wasna kungiyar kasar da suka mutu gaba daya, lokacin wnai hadarin jirgin sama a Gabon shekaru 19 da suka wuce. Idan kuwa aka dubi hakan, nasarar ta Zambia ta kawowa kasar da ma nahiyar Afrika baki daya babban abin farin ciki. Jaridar tace yan wasan na Zambia sun yi rawar gani, saboda a kan hanyar su ta samun wnanan nasara sai da suka kayar da kasashe kamar Senegal da Ghana da Cote d'Ivoire.