SiyasaAmurka
Amurka: Ganawar Trump da shugabannin Afirka
July 9, 2025Talla
Batun kasuwanci dai, na kan gaba cikin abubuwan da ake sa ran tattaunawar tasu za ta mayar da hankali. Shugaban Amurka Donald Trump ya gayyaci kasashen Senegal da Laberiya da Guinea-Bissau da Mauritania da kuma Gabon da dukan su ke gabar tekun Atlantica na Afirka, domin yin taro na musamman. Jami'an wadannan kasashen sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, suna tsammanin abubuwan da tattaunawar za ta mayar da hankali a kai sun hadar da batun kulla alakar kasuwanci da zuba jari da kuma tsaro. Sai dai har yanzu fadar ta White House ba ta yi wani karin haske a kan batutuwan da za su tattauna da wadannan kasashen Afirkan ba, nahiyar da tuni manyan abokan gabar Amurkan Rasha da Chaina suka yi ka'in da na'in a cikinta.