Rikice-rikiceGabas ta Tsakiya
Ko za a iya ceto wadanda Hamas ke garkuwa da su?
July 9, 2025Talla
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa, tattaunawar da suka yi da shugaban Amurka Donald Trump yayin ziyararsa ta mayar da hankali ne kan kokarin kwato Isra'ilawan da kungiyar Hamas ke garkuwa da su tun a watan Oktobar bara. Netanyahu ya wallafa a shafinsa na X cewa, sun kuma tattauna abubuwan da suka biyo baya da ma nasarorin da suka cimma kawo yanzu a rikicin kwanaki 12 da suka yi da Iran.