Akwai tasiri a ganawar Ramaphosa da Trump?
May 21, 2025Rahotanni sun nunar da cewa, Shugaba Donald Trump ya yi amfani da ganawar ta fadar White House wajen tunkarar Shugaba Ramaphosa tare da zargin kasarsa da kin dakatar da kisan fararen fata da ake yi zargin da Ramaphosa ya musanta. A wata hirar da ya yi da gidan talabijin din kasarsa gabanin tashinsa zuwa Washington, Ramaphosa ya nunar da cewa ko suna so ko ba sa so tilas suna jone da Amurka. Trump dai ya soke shirin agaji a Afirka ta Kudu tare da korar jakadanta a Amurka da kuma tayin mafaka ga fararen fatar kasar da ke zaman tsiraru, a wani mataki na mayar da martani kan gyaran dokokin mallakar filaye da kuma karar da Pretoria ta maka Isra'ila a kotun duniya sakamakon yakin yankin Zirin Gaza na Falasdinu. Amurka dai na zaman babbar abokiyar kasuwancin Afirka ta Kudu ta biyu, bayan kasar Chaina da ke kan sahun gaba.