Mahukuntan DRC da 'yan tawayen M23 za su fara tattaunawa
April 5, 2025Wannan tattaunawa da za a yi ta a ranar 9 ga watan Afirilu karkashin jagorancin mahukuntan Doha na zuwa ne bayan wacce suka yi a baya da ta kai ga nasarar janyewar 'yan tawayen daga wasu yankunan gabashin kasar kamar yadda wata majiya dake da kusanci da gwamnatin Kinsasha ta bayyana.
Kungiyar 'yan tawayen M23 mai samun goyon bayan Rwanda ta sha alwashin mutunta duk wata yarjejeniya da za a cimma a wanna zama dake tafe.
Tun bayan barkewar rikicin M23ta kwace iko da wurare masu arzikin ma'adinai karkashin kasa a hare-harenta lamarin da ya tilasta wa sama da mutum dubu 100,000 tserewa zuwa wasu kasashe makwabta.
Tun a watan Janairun shekarar nan ne dai rikici ya barke tsakanin dakarun gwamnati da na kungiyar M23, wanda Majalisar Dinkin Duniya da kasashen Yamma suka zargi makwabciyar kasar Ruwanda da tallafa wa 'yan tawayen da makamai.
Karin Bayani:AU ta yaba da zaman sulhu tsakanin DRC da Ruwanda a Qatar