Mahmud Abbas na son ganin karshen yakin Gaza
June 10, 2025A cikin wasikar da Shugaban Falasdinawa, Mahmud Abbas ya aike wa Shugaba Emmanuel Macron na Faransa da yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, Abbas ya ce, a shirye yake ya aika goron gayyatar turo dakarun kasashen larabawa da na kasa da kasa domin su kasance cikin shirin tabbatar da tsaro bisa sahalewar kwamittin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya. A cikin sanarwar da Fadar Elysee ta Faransa ta fitar, ta yi maraba da alkawuran da ba a taba gani ba, wanda ke nuna ainahin shirye-shiryen aiwatar da yarjejeniyar a tsakanin kasashen biyu.
Karin bayani: Shugabannin Larabawa sun hadu a kan yakin Gaza
Shugaba Macron ya ce, ya na da aniyar amincewa da kasar Falasdinu, amma kuma ya gindaya sharudda da dama da suka hada da kawo karshen Hamas. Sai dai kuma a wasikar, shugaban Falasdinu, Abbas ya jaddada aniyarsa na yin garambawul ga hukumar Falasdinawa da ma shirinsa na gudanar da zaben shugaban kasa a cikin shekara guda tare da taimakon kasashen duniya.