Mahawara ta kabre a Majalisar Dinkin Duniya
September 22, 2011Akasarin sharhunan da jaridun Israila suka wallafa a wannan Alhamis sun yaba matsayin shugaba Barack Obama game da yunkurin palesdinawa na samun kujera a Majalisar Dinkin Duniya. Jaridar Maariv da ke fitowa a ko wace rana ta Allah ta buga hoton ganawa tsakanin shugaban na Amirka da kuma firmainistan kasarsu Benjamin Netenyahu, tare da danganta shi da goyon bayan da ya fito daga Amirka. Sai dai kuma jaridar Haaretz ta nuna rashin jin dadainta da abin da ta kira, neman haddasa zaman kara zube tsakanin makota da ke gaba da juna da shugaban Amirka ke neman yi.
Su ma dai dubban palesdinawa sun gudanar da zanga zanga kama a Ramallah har zuwa Naplouse da ma dai gaban cibiyar Majalisar Dinkin Duniya, domin nuna bacin ransu game da in na´am da Obama ya yi da gaggwarmayar da suke yi na samon cikkaken 'yanci. Cikin rubuce da palesdinawa suka yi akan kwalaye da kuma kalaman batacin da suke yi ta rerawa, suka ce abin kunya na kasar Amirka da ke ikirarin bin tafarkin demokaradiya ta yi kememe da yunkurin Palesdinu na samun kujera a Majalisar Dinkin D.
To amma a wani mataki na kauce wa fito na fito, kasar faransa ta bayar da shawarar samar wa Palesdinu matsayin ''yar kallo a majalisar ta dinkin duniya. A ganin sumayya Farhat-naser wata yar palesdinu da ke da zanma a Ramallah, tayin Faransa wani ci gaba ne mai maana.
"Kwarai kuwa, wannan wata hobbasa da ta fito daga ƙasar faransa, za ta iya bayar da damar gano bakin zaren warware tankiyar. A wannan hali ko da Mahmoud Abbas ya shigar da bukatar gaban majalisar dinkin Duniya, za a shafe makwani kafin a kaɗa kuria domin a amincce da kudirin koko a´a. Amma kuma zai ci gaba da zama cikin agendar babban taron. zama yar kallo ma babban ci gaba ne domin zai bamu damar fara gina kasarmu."
Sai dai shugaban palesdinawa Mahmoud Abbas ya ce babu guda babu ja da baya a yunkurin da ya ke yi na shigar da bukatarsa gaban Majalisar. Ya zuwa yanzu dai kasashe shida ne dai suka bayyana aniyarsu ta kada kudirin amincewa da samar da Palesdinu mai cin gashin kanta. Amma kuma firaministan isra'ila Benjamin Netanyahu ya bi sahun Amirka wajen gindayawa Palesdinu sharadin kan teburin sulhu kafin a samar mata da kujera a MDD.ya ce palesɗinawa sun cancanci samun kasa mai cin gashin kanta. Amma kuma ya zama wajibi a garesu su koma kan teburin tattaunawa da Israila. Idan ba haka ba,haƙarsu ta samun kujera a majalisar dinkin duniya baa za ta cimma ruwa ba. A gani na palesɗinawa na neman ƙasashen duniya sun amince da yunkurinsu na kafa ƙasa Yantatta, amma kuma ba su da niyar cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Israila a ɗaya hannun.
Kasar Faransa da ke da kujerar dindindin a majalisar ta ki bayyana ko za ta kada kuri'ar amincewa da kudirin da Palesdinu ta shigar ko ko a'a. alhali ana sa ran matsayinta zai iya yi tasiri kan wasu mambobin kwamitin kamar gabon da Potugal da kuma bosniya. To amma Jamus za ta yi na ta jawabin ta ranar litinin mai zuwa idan Allah ya yarda. Ministan harkokinta na kasashen ketare Guido Westerwelle ya ce matsayin Amirka ya na kan turba.
"A nawa ra´ayin jawabin shugaban Amirka wata matashiya ce, domin ya kafa wani sabon tushe na samar da maslaha a rikicin yankin gabas ta tsakiya. Amma kuma ya warware duk wani shakku da ake da shi game da samar da haɗa ƙarfi da ƙarfe domin samar da ƙasashe biyu da ke daura da juna."
Duk da barazanar hawa kan kujerar naki da Amirka ke yi, kasashe Birtaniya da indiýa da kuma tarayyar najeriya da ke da kujera a kwamitin na sulhu ba su bayyana matsayinsu ba.
Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Yahouza Sadissou Madobi