Mahawara mai zafi kan yawan ziyarar Tinubu a Paris
April 2, 2025Kasar ta Faransa dai na zaman kasa mafi taka kafa ga shugaban da ke kara nuna alamar karkata cikin harkokinsa. Ya zuwa wata na Maris da ya shude dai, shugaban ya share kwanaki kusan 200 cikin wasu kasashe 19 da ziyarta sau dai dai har 30.
Kafin sabuwar ziyarar ta Faransa da ke zaman kasa mafi taka kafa ta shugaban kasar da ke daf da shiga shekaru guda biyu cikin wa'adin mulkinsa. Wata sanarwar fadar gwamnatin kasar dai ta ce shugaban zai kuma yi amfani da lokacin hutun nasa domin nazarin tasirin wasu cikin manufofi na gwamnatin da yake jagora, kafin kaiwa ya zuwa ga bikin cikarsa shekaru biyu yana kan mulki.
Tuni dai ziyarar tasa ke daukar hankali cikin kasar in da masu adawar tarayyar Najeriyar ke fadin da sauran sake. Kuma a tunanin Umar Sani dake zaman kakakin tsohon mataimaki na shugaban kasar, babu bukatar tafiya zuwa waje kafin neman samu na wurin hutawa.
Holewa a cikin sunan mulki, ko kuma kokari na badda kamanni dai, kama daga batu na lafiya ya zuwa neman cika ka'idar kaiwa ya zuwa ajiye ragamar mulki dai, ziyarar dai na kuma jawo kace-nace a tarrayar Najeriya.Har ya zuwa yanzun dai Tinubun bai taba gwada mika mulki ga mataimakinsa ba a cikin jerin tafiyar da ke zaman ba sabunba.
Koma ta ina masu adawar suke tunanin da biyu, hasashen nasu bai wuci kokari na adawar ba, a fadar Abdul Aziz Abdul Aziz dake zaman daya a cikin kakaki na shugaba Bola Ahmed Tinub.
Kundin tsarin mulki na kasar dai yayi fayyacin hanyoyin kaiwa ya zuwa ajiye mulki a banagre na shugaban kasar. Kuma sashi na 141 karamin sashe na daya da na biyu a fadar Barrista Mohammed Tudun Wada da ke zaman wani lauya mai zaman kansa a Najeriya bisa ka'idar ta karbar mulki a bangaren mataimaki na shugaban kasar.
Sannu a hankali dai yana zaman jiki tsakanin miliyoyi na 'yan kasar kai kawo na shugaban kasar zuwa kasar ta Faransa.