Mahakar zinari ta rufta da gomman mutane a Sudan
September 6, 2025Talla
Hukumomin Sudan na cewa hatsarin na wurin hakar zinari ya auku ne a yankin Um Aud da ke yammacin birnin Berber a kogin Nilu. Babban daractan birnin, Hassan Ibrahim Karar ya ce, ma'aikatan agaji na yin dukannin me yiwu wa wajen ganin sun ceto wadanda ake kyautata zaton suna da sauran numfashi.
Tun bayan barkewar fada tsakanin dakarun kasar da sojin RSF a shekarar 2023, dukannin bangarorin ke daukar nauyin rikicin ta hanyar ma'aikatar zinare ta kasar. Jami'ai da ma kungiyoyi masu zaman kansu na cewa, kusan dukannin gwala-gwalen ana tura su zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa da ake zargin ta na bai wa RSF makamai, zargin da ta musanta.