Gemeinsam aus der Krise
June 14, 2012Shugaban hukumar tarayyar Turai Jose Manuel Barroso, wanda ya yiwa majalisar dokokin tarayyar Turai jawabi, ya bayyana cewar a yanzu ne yafi dacewa Turai ta dunƙule wuri guda domin shawo kan matsalolin dake addabarta musamman dangane da kare darajar takardar kuɗin Euro, wadda ke fuskantar ƙalubale tun bayan da rikicin kuɗi ya tilastawa ƙasashen Girka da Portuagal da Ireland kana a baya bayannan da Spaniya neman ɗauki.
Mr Barroso ya bayyana buƙatar ɗaukar muhimman matakan da suka dace domin shawo kan matsalolin da a yanzu suka dabaibaye Turai, inda ya mayar da hankali ga buƙatar daidaita kasafin kuɗin Turai da kuma inganta harkokin bankunan ta hanyar samar da dokoki na bai ɗaya, lamarin da wasu ke ganin zai ci gaba da fuskantar turjiya daga gwamnatocin Turai daban daban da ba za su sami 'yancin yin gaban kansu ba kenan wajen neman rance, amma Barroso ya ce kasafin kuɗin zai anfani rukunin jama'a daban daban a tarayyar Turai:
" Ya ce muna buƙatar kawar da ruɗanin dake tattare da batun kasafin kuɗin tarayyar Turai da wasu ke ganin na cibiyarta dake birnin Brussels ne. Kasafin kuɗin tarayyar Turai na bunƙasa birane da yankuna da kuma karkarar mu ne. Kuɗi ne kuma da za'a yi anfani dashi wajen samar da kyakkyawar makoma ga Turai da kuma ga waɗanda suke sha'awar samun makoma ta gari a ƙungiyar."
Yarjejeniyar walwalar jama'a a Turai
Barroso ya kuma bayyana taƙaicin sa game da gaban kai da wasu ƙasashen Turai ke yi a baya bayannan wajen ɗaukar matakan kare kan iyakokin su daga zirga zirga a tsakanin rukunin ƙasashen Turai dake cikin yarjejeniyar Schengen da ta sahhalle walwala a tsakanin gamayyar ƙasashe wakilai a cikin ta:
" Ya ce ina mai taƙaici ga irin matakin da majalisar Turai ta ɗauka a baya bayannan akan shawarwarin da muka tsayar dangane da yankin Schengen ke ɗauka game da iyakokin su. Wannan mummunan mataki ne kuma a lokacin da bai dace ba bisa tubalin da muka gina Turai akansa."
Mafita ga rikicin kuɗi a Turai
Sai dai kuma wasu daga cikin 'yan majalisar Turai irinsu Joseph Daul dake jagorantar ɓangaren masu ra'ayin riƙau ya bayyana buƙatar sanin inda ƙungiyar ta dosa a dai dai lokacin da take fuskantar matsaloli iri-iri:
" Ya ce Wai shin muna da ƙarfin zuciya da hanzarin siyasa domin kare manufofin jam'iyyunmu akan 'yantacciyar siyasa ne, ko kuma zamu yi kamar yadda muka yi a shekaru biyun da suka gabata inda muke yin taruka daban daban domin samun mafita da kuma kyale dokoki da kasuwannin hannayen jari da zabin al'umma su kasance kan gaba da kuma bankuna?
Akwai dai wasu dake cewar idan har Turai na son bunƙasa to, kuwa tilas ne taci gaba da yin aiki da asusun bayar da rance ga ƙasashen da bashi ya yiwa katutu, kana bankin zuba jari na Turai da kuma babban bankin Turai su ƙara shiga a dama dasu wajen ƙoƙarin shawo kan matsalar rikicin kuɗi a yankin, inda Spaniya ta sami ɗauki ga bankunanta daga Turai, ɗaukin da kuma Martin Callanan na jam'iyyar masu ra'ayin riƙau daga Birtaniya ya ce ya gaza yin tasirin a zo a gani ga matsalar dake ci gaba da cin gungun ƙasashen na Turai, abinda ya ce a yi hattara dashi a dai dai lokacin da ƙungiyar ke cikin ruɗanin neman mafita ga darajar takardar kuɗin Euro, wadda kuma ƙasar sa ta Birtaniya ba ta cikin gamayyar.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasir Awal