Macron zai kai wa Issoufou Ziyara a Nijar
December 17, 2019Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron zai kai ziyarar aiki a birnin yamai a ranar Lahadi mai zuwa don ganawa da takwaran aikinsa na Nijar Mahamadou Issoufou, kwanaki kalilan bayan mummunar harin da 'yan ta'adda suka kai a sansanin sojoji na Inates wanda da ya salwantar da rayukan dakaru 71. Fadar mulki ta Elysee da ta bayar da wannan sanarwa ta ce sa'o'i kalilan Macron zai shafe a babban birnin na Nijar domin halatar bikin karrama sojojin da suka riga mu gidan gaskiya a filin daga.
Shi dai Macron zai fara ya da zango a Côte d' Ivoire a ranukan Jumma'a da Asabar kafin ya isa Jamhuriyar Nijar. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaba na Faransa ya tanadi taron kolin da takwarorinsu na kasashen Sahel a ranar 13 ga watan Janairu a birnin Pau da ke kudancin Faransa, domin tantance wajibcin janyewar sojojin Faransa ko ci gaba da yaki da ta'addanci a yankin sahel. Sojojin Faransa dubu hudu da 500 ke yaki da ta'addaci a yankin Sahel karkashin rundunar Barkhane.