SiyasaAfirka
Macron na jagorantar gangamin tallafawa Ukraine
March 27, 2025Talla
Shugabannin kasashe da gwamnatoci 27 ke halartar taron na birnin Paris ciki kuwa har da Firaministan Burtaniya Keir Starmer da ta Italiya Giorgia Meloni, har ma da mataimakin shugaban kasar Turkiyya Cevdet Yilmaz, wanda shi ne zai wakilci kasar dake da alaka ta kut-da-kut da kungiyar tsaro ta NATO, kasancewar shugaba Racep Tayyip Erdogan na fuskantar matsin lamba daga masu zanga-zangar kin jinin gwamnati.
Karin bayani: Ukraine da Rasha sun amince da tsagaita wuta a Bahar Maliya:
Macron da Starmer na fadi tashin shawo kan kasashen Turai kara tallafawa Ukraine, duk da cewa shugaban Amurka Donald Trump ya yi sanarwar bazata na jagorantar tattaunawar sulhu tsakanin Zelensky da takwaransa na Rasha Vladimir Putin.