Macron: Muna adawa da sake fasalin Gaza
April 7, 2025Talla
Ya ce sun yi watsi da korar jama'a daga yankinsu na asali da duk wata mamaya a Zirin Gaza da Yammacin Gabar Kogin Jordan, bayan ganawa da Shugaban Masar Abdel-Fatah al-Sissi a birnin Alkahira.
Shirye-shiryen mamaye zirin Gaza ko yammacin kogin Jordan ya sabawa dokar kasa da kasa in ji Macron, bisa la'akari da tsare-tsaren da Shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar a watan Fabrairu na sauyawa yankin fasali.
Kalaman Trump, wanda ya ba da shawarar sake tsugunar da Falastinawa miliyan 2 mazauna zirin Gaza, ya samu martanin fushi a tsakanin kasashen Larabawa. Bugu da kari shugaban na Faransa ya kuma soki sake barkewar rikicin a Gaza bayan karewar wa'adin tsagaita wuta na makonni shida a farkon wannan shekara.