Mace-mace a iftila'in ambaliya a Angola
April 20, 2021Talla
kamfanin dillancin labaran Angola ya ruwaito cewa an shafe kimanin sa'o'i bakwai ana ruwan sama a Luanda babban birnin kasar, lamarin da ya sa gadoji suka rushe, bishiyoyi suka tumbuke yayin da motocin da ke nutse a cikin ruwa. An ba da sanarwar mutuwar mutane 14 yayin da wasu iyalai dubu 8,000 suka rasa gidajensu sakamakon ambaliya da ta biyo bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya.
Mai magana da yawun Hukumar agajin gaggawa ta kasar Angola Faustino Minguês ya ce yawancin wadanda iftila'in ya shafa sun mutu ne bayan da bangon da ya ruguje ya fada a jikinsu ko kuma wutar lantarki ta yi ajalinsu.